waɗannan ƙungiyõyi biyu* ne mãsu husũma, sun yi husũma ga sha'anin Ubangijinsu. To, waɗanda suka kãfirta an yanka musu waɗansu tufafi daga wata irin wuta, anã zuba tafasasshen ruwa daga bisa kãwunansu.
____________________
* Kuma ya kasa mutãne ƙungiya biyu, ƙungiyar farko sũne mãsu bin addinin gaskiya, ƙungiya ta biyu sũ ne mãsu karkace wa addinin gaskiya, kamar kasũsuwa uku na farko. A kõ da yaushe akwai husũma a tsakãnin ƙungiyoyin biyu. Sa'an nan ya ambaci sakamakon ƙungiyar ƙarya ta farkon,.

الترجمة الهوساوية
۞هَٰذَانِ خَصۡمَانِ ٱخۡتَصَمُواْ فِي رَبِّهِمۡۖ فَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ قُطِّعَتۡ لَهُمۡ ثِيَابٞ مِّن نَّارٖ يُصَبُّ مِن فَوۡقِ رُءُوسِهِمُ ٱلۡحَمِيمُ
waɗannan ƙungiyõyi biyu ne mãsu husũma, sun yi husũma ga sha'anin Ubangijinsu. To, waɗanda suka kãfirta an yanka musu waɗansu tufafi daga wata irin wuta, anã zuba tafasasshen ruwa daga bisa kãwunansu.
Abubakar Mahmoud Gumi - Hausa translation